‏ Matthew 24:23-28

23A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata. 24Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 25Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.

26 “Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata. 27Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance. 28Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.
Copyright information for HauSRK