Matthew 24:29-31
(Markus 13.24-27; Luka 21.25-28)
29 “Nan da nan bayan tsabar wahalan nan “ ‘sai a duhunta rana,wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama,
za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’ ▼
▼ Ish 13.10; Ish 34.4
30 “A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma. 31Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.
Copyright information for
HauSRK