Matthew 24:32-35
(Markus 13.28-31; Luka 21.29-33)
32 “Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa. 33Haka kuma, sa’ad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa. 34Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru. 35Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.
Copyright information for
HauSRK