Matthew 27:27-30
Sojoji sun yi wa Yesu ba’a
(Markus 15.16-21; Yohanna 19.2,3)
27Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, sa’an nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi. 28Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga. 29Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” 30Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai.
Copyright information for
HauSRK