‏ Matthew 28:16-20

Babban umarni

(Markus 16.14-18; Luka 24.36-49; Yohanna 20.19-23; Ayyukan Manzanni 1.6-8)

16Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu. 17Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin
Ko kuwa cikin; dubi Ayy M 8.16; 19.5; Rom 6.3; 1Kor 1.13; 10.2 da Gal 3.27
sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki,
20kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”
Copyright information for HauSRK