‏ Matthew 3:13-17

Baftismar Yesu

(Markus 1.9-11; Luka 3.21,22)

13Sai Yesu ya zo daga Galili, ya je Urdun don Yohanna yă yi masa baftisma. 14Amma Yohanna ya so yă hana shi, yana cewa, “Ina bukata ka yi mini baftisma, yaya kake zuwa wurina?”

15Yesu ya amsa ya ce, “Bari yă zama haka yanzu; ya dace mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Sa’an nan Yohanna ya yarda.

16Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa. 17Sai murya daga sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai.”
Copyright information for HauSRK