Matthew 4:12-17
Yesu ya fara wa’azi
(Markus 1.14,15; Luka 4.14,15)
12Da Yesu ya ji labari cewa an kulle Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili. 13Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali 14don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, 15“Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali,da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun,
wannan yankin Galili ta Al’ummai,
16mutanen da suke zama cikin duhu
sun ga babban haske;
haske kuma ya haskaka
a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.” ▼
▼Ish 9.1,2f
17Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”
Copyright information for
HauSRK