Matthew 7:17-20
17Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da’ya’ya masu kyau. 18Itace mai kyau ba ya ba da munanan’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da’ya’ya masu kyau. 19Duk itacen da ba ya ba da’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta. 20Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”
Copyright information for
HauSRK