‏ Matthew 8:1-4

Mutum mai kuturta

(Markus 1.40-45; Luka 5.12-16)

1Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi. 2Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.”

3Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar
Girik aka tsabtacce
da shi daga kuturtarsa.
4Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.”
Copyright information for HauSRK