‏ Matthew 8:14-17

Yesu ya warkar da mutane da yawa

(Markus 1.29-34; Luka 4.38-41)

14Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi. 15Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima.

16Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ya ɗebi rashin lafiyarmu,
ya kuma ɗauki cututtukanmu.”
Ish 53.4

Copyright information for HauSRK