‏ Matthew 9:1-8

Yesu ya warkar da shanyayye

(Markus 2.1-12; Luka 5.17-26)

1Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya ƙetare ya zo garinsa. 2Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

3Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!”

4Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku? 5Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’ 6Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.” 7Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida. 8Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan.
Copyright information for HauSRK