‏ Micah 5

An yi alkawarin mai mulki daga Betlehem

1Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa,
Ko kuwa Ƙara ƙarfin katangarki, ya katangan birni

gama an kewaye mu da yaƙi.
Za su bugi kumatun mai mulkin
Isra’ila da sandar ƙarfe.

2“Amma ke, Betlehem ta Efrata,
ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki
Ko kuwa masu mulki
a Yahuda,
daga cikinki wani zai zo domina
wanda zai yi mulkin Isra’ila,
wanda asalinsa
Da Ibraniyanci fitowa daga

tun fil azal ne.”
Ko kuwa daga madawwamin kwanaki

3Saboda haka za a yashe Isra’ila
har sai wadda take naƙuda ta haihu
sauran’yan’uwansa kuma sun dawo
su haɗu da Isra’ilawa.

4Zai tsaya yă yi kiwon garkensa
da ƙarfin Ubangiji,
cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa.
Za su kuma zauna lafiya, gama girmansa
za tă kai har ƙarshen duniya.

5Zai kuma zama salamarsu.
Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu hari
suka tattake kagarunmu,
za mu tā da makiyaya bakwai,
har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su.
6Za su yi mulkin
Ko kuwa ragargaza
ƙasar Assuriya da takobi,
ƙasar Nimrod kuma da zaran takobi.
Ko kuwa Nimrod a bakin ƙofofinta

Zai cece mu daga hannun Assuriyawa
sa’ad da suka kawo wa ƙasarmu hari
suka kuma tattake zuwa cikin iyakokinmu.

7Raguwar Yaƙub za tă kasance
a tsakiyar mutane masu yawa
kamar raɓa daga Ubangiji,
kamar yayyafi a kan ciyawa,
wanda ba ya jiran mutum
ko kuma yă dakata wa ɗan adam.
8Raguwar Yaƙub za tă kasance tare da al’ummai,
a cikin mutane masu yawa,
kamar zaki a cikin sauran namun jeji,
kamar ɗan zaki cikin garken tumaki,
wanda yake tattaka yă kuma yi kaca-kaca da su sa’ad da yake ratsa a cikinsu,
ba kuwa wanda zai cece su.
9Za a ɗaga hannunka cikin nasara a kan abokan gābanka,
za a hallaka maƙiyanka duka.

10“A wannan rana,” in ji Ubangiji “Zan hallaka dawakanku daga cikinku,
in kuma rurrushe kekunan yaƙinku.
11Zan hallaka biranen ƙasarku
in yi rugu-rugu da dukan katangunku.
12Zan kawar da maitarku,
ba za a ƙara yin sihiri ba.
13Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa
da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku,
nan gaba ba za ku ƙara rusuna
wa aikin hannuwanku ba.
14Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asheranku
Wato, alamar alliyar Ashera

in kuma rurrushe biranenku.
15Zan yi ramuwa cikin fushi da hasala
a kan al’umman da ba su yi mini biyayya ba.”
Copyright information for HauSRK