Numbers 28:1-8
Hadayu na kullayaumi
(Fitowa 29.38-43; Firistoci 6.8-13)
1Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 2“Ka umarci Isra’ilawa cewa, ‘Ku tabbatar kun miƙa mini hadaya ta abinci ta wuta mai daɗin ƙanshi a gare ni, a daidai lokaci.’ 3Ka gaya musu, ‘Ga hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, da za ku miƙa wa Ubangiji, raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya, marasa lahani. 4A miƙa rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma, 5tare da hadaya ta lallausan gari kashi ɗaya bisa goma na efan, kwaɓaɓɓe da kwalaba ɗaya na man zaitun mafi kyau. 6Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. 7Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki. 8Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa shi da yamma, tare irin hadaya ta lallausan gari, da hadaya ta sha da ka yi da safe. Wannan hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Copyright information for
HauSRK