‏ Numbers 29:1-6

Bikin Ƙahoni

(Firistoci 23.23-25)

1“ ‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni. 2Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda,’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji, duka su kasance marasa lahani. 3Tare da bijimin za a kuma miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; 4kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. 5A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara. 6Waɗannan ƙari ne ga hadayun ƙonawa na wata-wata da na kullayaumi, tare da hadayun garinsu da hadayun sha yadda aka tsara. Hadayu ne da aka miƙa wa Ubangiji ta wuta don daɗin ƙanshi.
Copyright information for HauSRK