‏ Numbers 35:9-15

(Maimaitawar Shari’a 19.1-13; Yoshuwa 20.1-9)

9Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, 10“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana, 11ku zaɓi waɗansu garuruwan da za su zama biranen mafakarku, inda wanda ya kashe mutum cikin kuskure zai iya gudu zuwa. 12Za su zama wuraren mafaka daga hannun mai bin hakki, don kada a kashe mai kisankai, tun ba a kai shi gaban shari’a, a gaban taron jama’a ba. 13Waɗannan garuruwa shida da aka bayar za su zama biranen mafakarku. 14A ba da uku a wannan gefe na Urdun, a kuma ba da uku a Kan’ana, su zama biranen mafaka. 15Waɗannan garuruwa shida za su zama wurin mafaka wa Isra’ilawa, baƙi da duk sauran mutanen da suke zama a cikinsu, saboda duk wanda ya kashe mutum cikin kuskure yă iya gudu zuwa.
Copyright information for HauSRK