Proverbs 13
1Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa,amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.
2Daga abin da ya fito leɓunan mutum ne mutum kan ji daɗin abubuwa masu kyau,
amma marar aminci yakan ƙosa ya tā-da-na-zaune-tsaye.
3Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa,
amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci.
4Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome,
amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.
5Adali yana ƙin abin da yake ƙarya,
amma mugu kan jawo kunya da ƙasƙanci.
6Adalci yakan lura da mutum mai mutunci,
amma mugunta takan sha kan mai zunubi.
7Wani mutum yakan ɗauki kansa mai arziki ne, alhali ba shi da kome,
wani ya ɗauki kansa shi matalauci ne, alhali shi mawadaci ne ƙwarai.
8Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa,
amma matalauci ba ya jin barazana.
9Hasken masu adalci kan haskaka ƙwarai,
amma fitilar mugaye mutuwa take.
10Girmankai kan jawo faɗa ne kawai,
amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.
11Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri,
amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
12Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo,
amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
13Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa,
amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada.
14Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne,
mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.
15Fahimta mai kyau kan sami tagomashi,
amma hanyar marar aminci tana da wuya.
16Kowane mai azanci yakan nuna sani,
amma wawa yakan yi tallen wawancinsa.
17Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala,
amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa.
18Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya,
amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.
19Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai,
amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta.
20Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima,
amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
21Rashin sa’a kan fafare mai zunubi,
amma wadata ce ladar adali.
22Mutumin kirki kan bar gādo wa’ya’ya’ya’yansa,
amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci.
23Gonar matalauci za tă iya ba da abinci a yalwace,
amma rashin adalci kan share shi tas.
24Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba,
amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.
25Masu adalci sukan ci isashen abinci,
amma cikin mugaye na fama da yunwa.
Copyright information for
HauSRK