Proverbs 17
1Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiruda ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.
2Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya,
kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin’yan’uwansa.
3Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta,
amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.
4Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna;
maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.
5Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne;
duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi.
6Jikoki rawanin tsofaffi ne,
kuma iyaye su ne abin taƙamar’ya’yansu.
7Leɓunan basira ba su dace da wawa ba,
ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya!
8Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi;
ko’ina ya juye, yakan yi nasara.
9Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne,
amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.
10Tsawata kan sa mutum ya koyi basira
fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.
11Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah;
za a aika manzo mutuwa a kansu.
12Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa’ya’ya
fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa.
13In mutum ya sāka alheri da mugunta,
mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba.
14Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne,
saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.
15Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci,
Ubangiji ya ƙi su biyu.
16Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa,
da yake ba shi da sha’awar samun hikima?
17Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe,
ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.
18Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani
ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci.
19Duk mai son faɗa yana son zunubi,
duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka.
20Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba;
duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala.
21Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki
babu farin ciki ga mahaifin wawa.
22Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,
amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
23Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce
don yă lalace yin adalci.
24Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima,
amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya.
25Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa
da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.
26Ba shi da kyau a hukunta marar laifi,
ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu.
27Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi,
mutum mai basira kuma natsattse ne.
28Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne,
da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.
Copyright information for
HauSRK