Proverbs 18
1Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai;yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai.
2Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta
amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.
3Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo,
haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo.
4Kalmomin bakin mutum suna da zurfi kamar ruwaye,
amma maɓulɓulan hikima rafi ne mai gudu.
5Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri
ko ka hana wa marar laifi adalci.
6Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa,
bakinsa kuma kan gayyaci dūka.
7Bakin wawa lalatar da kansa yake yi
leɓunansa kuma tarko ne ga ransa.
8Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke;
sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.
9Wanda yake ragwanci a aikinsa
ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.
10Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi;
masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
11Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga;
suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba.
12Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai,
amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
13Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara,
wannan wauta ce da kuma abin kunya.
14Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo,
amma in ya karai, to, tasa ta ƙare.
15Zuciya mai la’akari kan nemi sani;
kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya.
16Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa
yakan kuma kai shi a gaban babban mutum.
17Wanda ya fara mai da jawabi yakan zama kamar shi ne mai gaskiya,
sai wani ya fito ya yi masa tambaya tukuna.
18Jefa ƙuri’a kan daidaita tsakanin masu faɗa
ta kuma ajiye masu faɗan a rabe.
19Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa,
kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.
20Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika;
girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi.
21Harshe yana da ikon rai da mutuwa,
kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.
22Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau
ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
23Matalauci kan yi roƙo da taushi,
amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya.
24Mutum mai abokai masu yawa kan lalace,
amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.
Copyright information for
HauSRK