Proverbs 20
1Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne;duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.
2Fushin sarki yana kama da rurin zaki;
duk wanda ya sa shi fushi zai rasa ransa.
3Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa,
amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.
4Rago ba ya noma a lokacin noma;
saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.
5Manufofin zuciyar mutum zurfafan ruwaye ne,
amma mutum mai basira yakan jawo su.
6Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne,
amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda.
7Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi;
masu albarka ne’ya’yan da za su biyo bayansa.
8Sa’ad da sarki ya zauna kan kujerarsa don yă yi shari’a,
yakan ga dukan mugunta da idanunsa.
9 ▼
▼20:9, 20:20-20:22 a yawancin Littafi Mai Tsarki.
Wa zai iya cewa, “Na kiyaye zuciyata da tsarki;ni mai tsabta ne marar zunubi kuma”?
10Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba,
Ubangiji ya ƙi su duka.
11Akan san ƙananan yara ta ayyukansu,
ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta.
12Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani,
Ubangiji ne ya yi su duka.
13Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce;
ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.
14“Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya;
sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki.
15Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace,
amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja.
16A karɓi rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo;
a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
17Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi,
amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi.
18Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara;
in kana yaƙi, ka sami bishewa.
19Mai gulma yakan lalace yarda;
saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu.
20In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa,
fitilarsa za tă mutu a tsakiyar duhu.
21Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa
ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba.
22Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!”
Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka.
23 Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba,
da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.
24 Ubangiji ne yake bi da matakan mutum,
Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa?
25Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani
daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.
26Sarki mai hikima yakan gane mugunta;
ya hukunta su ba tausayi.
27Fitilar Ubangiji kan bincika zuciyar mutum
takan bincika lamirinsa.
28Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya;
ta wurin ƙauna sarautarsa za tă zauna a kafe.
29Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu,
furfura ita ce darajar tsofaffi.
30Naushi da rauni kan share mugunta,
dūka kuma kan tsabtacce lamiri.
Copyright information for
HauSRK