‏ Proverbs 22

1An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa;
tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.

2Mawadaci da matalauci suna da abu guda.
Ubangiji ne Mahaliccinsu duka.

3Mai basira kan ga damuwa tana zuwa yă nemi mafaka,
amma marar azanci kan yi ta tafiya yă kuma sha wahala.

4Sauƙinkai da tsoron Ubangiji
sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.

5A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko,
amma duk wanda ya kiyaye ransa kan kauce musu.

6Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

7Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci,
mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.

8Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala,
za a kuma hallaka sandar fushinsa.

9Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka,
gama yakan raba abincinsa da matalauta.

10Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje;
fitina da zargi kuma za su ƙare.

11Duk mai son tsabtar zuciya wanda kuma jawabinsa mai alheri ne
zai zama aminin sarki.

12Idanun Ubangiji na lura da sani,
amma yakan ƙi kalmomin marar aminci.

13Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!”
Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”

14Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi;
duk wanda yake a ƙarƙashin fushin Ubangiji zai fāɗa a ciki.

15Wauta tana da yawa a zuciyar yara,
amma sandar horo zai kore ta nesa da su.

16Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta
kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.

Maganganu Masu Hikima

Faɗi 1

17Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima;
ka yi amfani da abin da nake koyarwa,
18gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka
ka kuma kasance da su a shirye a leɓunanka.
19Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji,
ina koya maka yau, har kai ma.
20Ban rubuta maka maganganu talatin ba,
maganganun shawara da sani,
21ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai,
saboda ka iya ba da amsa daidai
ga duk wanda ya aike ka?

Faɗi 2

22Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta
kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a,
23gama Ubangiji zai yi magana dominsu
zai kuwa washe waɗanda suka washe su.

Faɗi 3

24Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai,
kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,
25in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa
ka kuma sa kanka a tarko.

Faɗi 4

26Kada ka zama mai ɗaukar lamuni
ko ka ba da jingina saboda bashi;
27gama in ka kāsa biya
za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.

Faɗi 5

28Kada ka matsar da shaidar kan iyakar
da kakanninka suka kafa.

Faɗi 6

29Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa?
Zai yi wa sarakuna hidima;
ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba.
Copyright information for HauSRK