Proverbs 25
Ƙarin karin maganar Solomon
1Waɗannan ƙarin karin maganar Solomon ne waɗanda mutanen Hezekiya sarkin Yahuda suka tara. 2Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun;a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne.
3Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi,
haka zukatan sarakuna suka wuce a bincika.
4Ka tace azurfa
sai kayan su fito don maƙerin azurfa;
5ka cire mugaye daga gaban sarki,
kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci.
6Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki,
kada kuma ka nemi wa kanka wuri a cikin manyan mutane;
7gara ya ce maka, “Ka hauro nan,”
da a ƙasƙantar da kai a gaban wani mai makami.
Abin da ka gani da idanunka
8kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa,
gama me za ka yi a ƙarshe
in maƙwabcinka ya ba ka kunya?
9In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama,
kada ka tona asirin wani,
10in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka
ba za ka kuma taɓa rabuwa da wannan mummuna suna ba.
11Kalmar da aka faɗa daidai
tana kamar zubin zinariyar da aka yi a mazubin azurfa.
12Kamar’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla
haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa.
13Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi
haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika;
ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi.
14Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama
haka mutumin da yake fariya a kan kyautan da ba ya bayarwa.
15Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki,
magana mai hankali kan karye ƙashi.
16In ka sami zuma, ka sha isashe kawai,
in ya yi yawa, za ka yi amai.
17Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka
yawan ganinka zai sa ya ƙi ka.
18Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini
haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa.
19Kamar haƙori mai ciwo ko yin tafiya da gurguwar ƙafa
haka yake ga mai dogara da marasa aminci a lokacin wahala.
20Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi,
ko kuwa kamar zuba ruwan tsami a kanwa,
haka yake da mai rera waƙoƙi ga mai baƙin ciki.
21In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci;
in yana jin ƙishi, ka ba shi ruwa ya sha.
22Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa,
Ubangiji kuma zai sāka maka.
23Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama,
haka jita-jita kan kawo fushi.
24Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki
da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
25Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji
haka yake da jin labari mai daɗi daga ƙasa mai nisa.
26Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace
haka yake da mai adalci wanda ya miƙa wuya ga mugaye.
27Ba shi da kyau ka sha zuma da yawa,
haka ma ba shi da kyau ka nemi girma wa kanka.
28Kamar birni da katangarsa sun rushe
haka yake da mutumin da ba ya iya danne fushinsa.
Copyright information for
HauSRK