‏ Proverbs 26

1Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi,
haka girmamawa bai dace da wawa ba.
2Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya,
haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take.
3Bulala don doki, linzami don jaki,
sanda kuma don bayan wawaye!
4Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa,
in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa.
5Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa,
in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne.
6Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi
haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa.
7Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas
haka karin magana yake a bakin wawa.
8Kamar ɗaura dutse a majajjawa
haka yake da girmama wawa.
9Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu
haka karin magana yake a bakin wawa.
10Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni
haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.
11Kamar yadda kare kan koma ga amansa,
haka wawa kan maimaita wautarsa.
12Gwamma riƙaƙƙen wawa
da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.

13Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya,
zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”
14Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa,
haka rago yake jujjuya a gadonsa.
15Rago kan sa hannunsa a kwano
ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.
16Rago yana gani yana da hikima
fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.

17Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa
haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa.

18Kamar yadda mahaukaci yake harbin
cukwimai ko kibiyoyi masu dafi
19haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci
sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!”

20In ba itace wuta takan mutu;
haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.
21Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta,
haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.
22Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi;
sukan gangara can cikin cikin mutum.

23Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba
haka leɓuna masu mugun zuciya.
24Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa,
amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci
25Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi,
gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.
26Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya,
duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.
27In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki;
in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.
28Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai,
daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.
Copyright information for HauSRK