Proverbs 3
Ƙarin ribar hikima
1Ɗana, kada ka manta da koyarwata,amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,
2gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa
su kuma kawo maka wadata.
3Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai;
ka ɗaura su kewaye da wuyanka,
ka rubuta su a allon zuciyarka.
4Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau
a gaban Allah da kuma a gaban mutane.
5Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe. ▼
▼Ko kuwa zai nuna maka hanyoyi
7Kada ka zama mai hikima a ganinka;
ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
8Wannan zai ba wa jikinka lafiya
yă kuma adana ƙasusuwanka.
9Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka,
ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
10ta haka rumbunanka za su cika har su zuba,
randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.
11Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji
kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,
12domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,
kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.
13Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima,
mutumin da ya sami fahimi,
14gama ta fi azurfa riba
tana kuma da amfani fiye da zinariya.
15Ta fi lu’ulu’u daraja;
ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.
16Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama;
a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.
17Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi,
dukan hanyoyinta kuma salama ne.
18Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta;
waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.
19Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya,
ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;
20ta wurin sani aka rarraba zurfafa,
gizagizai kuma suka zubo raɓa.
21Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira,
kada ka bar su su rabu da kai;
22za su zama rai a gare ka,
abin adon da zai gyara wuyanka.
23Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya,
ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;
24sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;
sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.
25Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya
ko lalacin da yakan auka wa mugaye,
26gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka
zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.
27Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace,
sa’ad da kana iya yin haka.
28Kada ka ce wa maƙwabcinka
“Ka yă dakata sai gobe,”
idan kana iya taimakonsa yanzu.
29Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka,
wanda yake zama da aminci kusa da kai.
30Kada ka zargi mutum ba dalili,
sa’ad da bai yi laifi ba.
31Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye
ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu.
32Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta
amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi.
33La’anar Ubangiji tana a gidan mugaye,
amma yakan albarkaci gidan adali.
34Yakan yi wa masu girman kai ba’a
amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri.
35Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna,
amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.
Copyright information for
HauSRK