‏ Proverbs 4

Hikima ce mafi girma duka

1Ku saurara’ya’yana ga koyarwar mahaifinku;
ku mai da hankali, ku sami fahimi.
2Ina ba ku sahihiyar koyarwa,
saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.
3Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina,
yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,
4ya koya mini ya ce,
“Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka;
ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.
5Ka nemi hikima, ka nemi fahimi;
kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.
6Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka;
ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.
7Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima.
Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.
8Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka;
ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka.
9Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka
tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.”

10Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa,
shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa.
11Na bishe ka a hanyar hikima
na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi.
12Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe;
sa’ad da kake gudu, ba za ka fāɗi ba.
13Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce;
ka tsare shi sosai, gama ranka ne.
14Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye
kada ka bi gurbin mugaye.
15Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta;
juya daga gare ta ka yi tafiyarka.
16Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta;
ba su barci sai sun cuci wani.
17Mugunta da ta’adi
kamar ci da sha suke a gare su.

18Hanyar adali kamar fitowar rana ce,
sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka.
19Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne;
ba sa sanin abin da ya sa suke tuntuɓe.

20Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa,
ka saurara sosai ga kalmomina.
21Kada ka bari su rabu da kai,
ka kiyaye su a cikin zuciyarka;
22gama rai ne ga waɗanda suke nemansu
da kuma lafiya ga dukan jikin mutum.
23Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka,
gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.
24Ka kau da muguwar magana daga bakinka;
ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka.
25Bari idanunka su dubi gaba sosai,
ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.
26Ka san inda ƙafafunka suke takawa
ka bi hanyoyin da suke daram kawai.
27Kada ka kauce dama ko hagu;
ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.
Copyright information for HauSRK