Proverbs 5
Gargaɗi a kan zina
1Ɗana, ka mai da hankali ga hikimataka saurara da kyau ga kalmomin basirata,
2don ka ci gaba da yin kome daidai
leɓunanka za su adana sani.
3Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma,
maganarta tana da sulɓi fiye da mai;
4amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya,
mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.
5Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa;
sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari.
6Ba ta wani tunanin rayuwa;
hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.
7Yanzu fa,’ya’yana, ku saurare ni;
kada ku juye daga abin da nake faɗa.
8Ku yi nesa da hanyarta,
kana ku je kusa da ƙofar gidanta,
9don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu
da kuma shekarunku ga wani marar imani,
10don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku
wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.
11A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi,
sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.
12Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo!
Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!
13Ban yi biyayya da malamaina ba
ko in saurari masu koyar da ni.
14Na zo gab da hallaka gaba ɗaya
a tsakiyar dukan taron.”
15Ku sha ruwa daga tankinku,
ruwa mai gudu daga rijiyarku.
16In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje,
rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?
17Bari su zama naka kaɗai,
don kada ka raba da baƙi.
18Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka,
bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.
19Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,
bari mamanta su ishe ka kullum,
bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.
20Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali?
Don me za ka rungume matar wani?
21Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji,
yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.
22Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi;
igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan.
23Zai mutu saboda rashin ɗa’a
yawan wawancinsa zai sa yă kauce.
Copyright information for
HauSRK