‏ Proverbs 7

Gargaɗi A kan mazinaciya

1Ɗana, ka kiyaye kalmomina
ka kuma ajiye umarnaina a cikinka.
2Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu;
ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka.
3Ka daure su a yatsotsinka;
ka rubuta su a allon zuciyarka.
4Ka faɗa wa hikima, “Ke’yar’uwata ce,”
ka kuma kira fahimi danginka;
5za su kiyaye ka daga mazinaciya,
daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali.

6A tagar gidana
na leƙa ta labule mai rammuka.
7Sai na gani a cikin marasa azanci,
na lura a cikin samari,
wani matashi wanda ba shi da hankali.
8Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta,
yana tafiya a gefen wajen gidanta
9da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa,
yayinda duhun dare yana farawa.

10Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi,
saye da riga kamar karuwa shirye kuma don ta yaudare shi.
11(Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya,
ƙafafunta ba sa zama a gida;
12wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali,
tana yawo a kowace kusurwa.)
13Sai ta kama shi ta rungume shi
da duban soyayya a fuskarta ta ce,

14“Ina da hadaya ta salama a gida;
yau zan cika alkawarina.
15Saboda haka na fito don in sadu da kai;
na neme ka na kuma same ka!
16Na lulluɓe gadona
da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.
17Na yayyafa turare a gadona
da mur, aloyes da kuma kirfa.
18Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe;
bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna!
19Mijina ba ya gida;
ya yi tafiya mai nisa.
20Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi
ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”

21Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce;
ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.
22Nan take, ya bi ta
kamar saniyar da za a kai mayanka,
kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo
23sai da kibiya ta soki hantarsa,
kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko,
ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.

24Yanzu fa,’ya’yana, ku saurare ni;
ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.
25Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta
ko ku kauce zuwa hanyoyinta.
26Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci;
kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.
27Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari
mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.
Copyright information for HauSRK