‏ Proverbs 8

Kiran hikima

1Hikima ba ta yin kira ne?
Fahimi ba ya tā da muryarsa ne?
2A ƙwanƙoli a kan hanya,
inda hanyoyi suka haɗu, ta ɗauki matsayinta;
3kusa da ƙofofin shiga cikin birni,
a mashigai, ta tā da murya,
4“Gare ku, ya mutane, nake kira;
na tā da muryata ga dukan’yan adam.
5Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali;
ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi.
6Ku saurara, gama ina da abubuwa masu darajan da zan faɗa;
na buɗe leɓunana don in faɗa abin da yake daidai.
7Bakina yana magana abin da yake gaskiya,
gama leɓunana sun ƙi mugunta.
8Dukan kalmomin bakina suna da adalci;
babu waninsu da ya karkace ko kuwa ƙarya ne.
9Ga mai tunani dukansu daidai ne;
ba su da laifi ga waɗanda suke da sani.
10Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa,
sani a maimakon zinariya zalla,
11gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja,
kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita.

12“Ni, hikima, ina zama tare da hankali;
ina da sani da iya rarrabewa.
13Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta;
ina ƙin girman kai da fariya,
halin mugunta da kuma muguwar magana.
14Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne;
ina da fahimi da kuma iko.
15Ta wurina sarakuna suke mulki
masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci;
16ta wurina sarakuna suke mulki,
da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.
17Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata,
kuma waɗanda suke nemana sukan same ni.
18Tare da ni akwai wadata da girmamawa,
dukiya da wadata masu dawwama.
19’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla;
amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau.
20Ina tafiya a hanyar adalci,
a kan hanyoyin gaskiya,
21ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata
ina sa wuraren ajiyarsu su cika.

22Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa,
kafin ayyukansa na tuntuni;
23an naɗa ni tun fil azal,
daga farko, kafin duniya ta kasance.
24Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni,
sa’ad da babu maɓulɓulai masu ruwa;
25kafin a kafa duwatsu a wurarensu,
kafin tuddai ma, an haife ni,
26kafin ya yi duniya ko gonaki
ko wata ƙurar duniya.
27Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu,
sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa,
28sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa
ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram,
29sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa
domin kada ruwaye su zarce umarninsa,
da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya.
30A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa.
Na cika da murna kowace rana,
kullum ina farin ciki a gabansa,
31ina farin ciki da dukan duniyarsa
ina murna da’yan adam.

32“Yanzu fa,’ya’yana, ku saurare ni;
masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.
33Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima;
kada ku ƙyale ta.
34Mai albarka ne wanda ya saurare ni;
yana tsaro kullum a ƙofofina,
yana jira a ƙofar shigata.
35Gama duk wanda ya same ni ya sami rai
zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
36Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa;
dukan waɗanda suke ƙina suna ƙaunar mutuwa ke nan.”
Copyright information for HauSRK