Proverbs 9
Gayyatar hikima da gayyatar wawanci
1Hikima ta gina gidanta;ta yi ginshiƙansa bakwai.
2Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta;
ta kuma shirya teburinta.
3Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira
daga wurare masu tsayi na birnin.
4“Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!”
Tana faɗa wa marasa hankali.
5“Ku zo, ku ci abincina
da ruwan inabin da na gauraye.
6Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu;
yi tafiya a hanyar fahimi.
7“Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi
duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci.
8Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka;
ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.
9Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima;
ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa.
10“Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,
sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
11Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa,
za a kuwa ƙara wa ranka shekaru.
12In kana da hikima, hikimarka za tă ba ka lada;
in kai mai ba’a ne, kai kaɗai za ka sha wahala.”
13Wawancin mace a bayyane yake;
ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani.
14Takan zauna a ƙofar gidanta,
a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni,
15tana kira ga masu wucewa,
waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.
16“Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!”
Tana ce wa marasa hankali.
17“Ruwan da aka sata ya fi daɗi;
abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”
18Amma ba su san cewa matattu suna a can ba,
cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba.
Copyright information for
HauSRK