Psalms 100
Zabura ce. Don yin godiya. 1Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.2Yi wa Ubangiji sujada da murna;
ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.
3Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah.
Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;
mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.
4Ku shiga ƙofofinsa da godiya
filayen gidansa kuma da yabo;
ku gode masa ku kuma yabi sunansa.
5Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada;
amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.
Copyright information for
HauSRK