Psalms 101
Ta Dawuda. Zabura ce. 1Zan rera wa ƙauna da adalcinka;gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo.
2Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi,
yaushe za ka zo gare ni?
Zan bi da sha’anin gidana
da zuciya marar abin zargi
3Ba zan kafa a gaban idanuna 1
wani abu marar kyau ba.
Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci;
ba za su manne mini ba.
4Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni;
ba abin da zai haɗa ni da mugunta.
5Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye
shi za a kashe;
duk mai renin wayo da mai girman kai,
ba zan jure masa ba.
6Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar,
don su zauna tare da ni;
tafiyarsa ba ta da zargi
zai yi mini hidima.
7Babu mai ruɗun
da zai zauna a gidana;
babu mai ƙaryan
da zai tsaya a gabana.
8Kowace safiya zan rufe bakunan
dukan mugaye a ƙasar;
zan yanke kowane mai aikata mugunta
daga birnin Ubangiji.
Copyright information for
HauSRK