‏ Psalms 103

Ta Dawuda.

1Yabi Ubangiji, ya raina;
dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.
2Yabi Ubangiji, ya raina,
kada kuma ka manta dukan alheransa,
3wanda yake gafarta dukan zunubai
yake kuma warkar da dukan cututtuka,
4wanda ya fanshi ranka daga rami
ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,
5Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau
domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.

6 Ubangiji yana aikata adalci
da kuma gaskiya ga duk waɗanda aka danne.

7Ya sanar da hanyoyinsa wa Musa,
ayyukansa ga mutanen Isra’ila.
8 Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri,
mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.
9Ba zai yi ta zargi ba
ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;
10ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu
ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.
11Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya,
haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;
12kamar yadda gabas yake daga yamma,
haka ya cire laifofinmu daga gare mu.

13Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin’ya’yansa,
haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;
14gama ya san yadda aka yi mu,
ya tuna cewa mu ƙura ne.
15Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa
da suke haɓaka kamar fure a gona;
16iska kan hura a kansa sai ya ɓace
ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake.
17Amma daga madawwami zuwa madawwami
ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa,
adalcinsa kuma tare da’ya’yansu,
18tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa
suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.

19 Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama,
masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka.

20Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa,
ku jarumawa masu yi masa aiki,
waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.
21Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama,
ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.
22Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa
ko’ina a mulkinsa.

Yabi Ubangiji, ya raina.
Copyright information for HauSRK