Psalms 105
1Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
2Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.
3Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki;
bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
4Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
5Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi,
mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar,
6Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa,
Ya ku’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa.
7Shi ne Ubangiji Allahnmu;
kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya.
8Yana tuna da alkawarinsa har abada,
maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,
9alkawarin da ya yi da Ibrahim,
rantsuwar da ya yi wa Ishaku.
10Ya tabbatar da shi ga Yaƙub a matsayin ƙa’ida,
Isra’ila a matsayin madawwamin alkawari,
11“Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana
a matsayin rabo za ka yi gādo.”
12Sa’ad da suke kima kawai,
kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,
13suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma,
daga masarauta zuwa wata.
14Bai bar kowa yă danne su ba;
saboda su, ya tsawata wa sarakuna,
15“Kada ku taɓa shafaffena;
kada ku yi wa annabawa lahani.”
16Ya sauko da yunwa a kan ƙasa
ya kuma lalace dukan tanadinsu na abinci;
17ya kuma aiki mutum a gabansu,
Yusuf, da aka sayar a matsayin bawa.
18Suka raunana ƙafafunsa da sarƙa
aka sa wuyansa cikin ƙarafa,
19sai abin da ya rigafaɗi ya cika
sai da maganar Ubangiji ta tabbatar da shi mai gaskiya.
20Sarki ya aika aka kuma sake shi,
mai mulkin mutane ya’yantar da shi.
21Ya mai da shi shugaban gidansa,
mai mulki a bisa dukan abin da ya mallaka,
22don yă umarci sarakunansa yadda ya ga dama
yă kuma koya wa dattawa hikima.
23Sa’an nan Isra’ila ya shiga Masar;
Yaƙub ya yi zama kamar baƙo a ƙasar Ham.
24 Ubangiji ya mai da mutanensa suka yi ta haihuwa;
ya sa suka yi yawa suka fi ƙarfin maƙiyansu,
25waɗanda ya juya zukatansu su ƙi mutanensa
don su haɗa baki a kan bayinsa.
26Ya aiki Musa bawansa,
da Haruna, wanda ya zaɓa.
27Suka yi mu’ujizansa a cikinsu,
abubuwan mamakinsa a cikin ƙasar Ham.
28Ya aiko da duhu ya kuma sa ƙasar tă yi duhu,
ba domin sun yi tawaye a kan maganarsa ba?
29Ya mai da ruwaye suka zama jini,
ya sa kifayensu suka mutu.
30Ƙasarsu ta yi ta fid da kwaɗi,
waɗanda suka haura cikin ɗakunan kwana na masu mulkinsu.
31Ya yi magana, sai tarin ƙudaje suka fito,
cinnaku kuma ko’ina a ƙasar.
32Ya mai da ruwan samansu ya zama ƙanƙara,
da walƙiya ko’ina a ƙasarsu;
33ya lalace inabinsu da itatuwan ɓaurensu
ya ragargaza itatuwan ƙasarsu.
34Ya yi magana, sai fāri ɗango suka fito,
fāran da ba su ƙidayuwa;
35suka cinye kowane abu mai ruwan kore a cikin ƙasarsu,
suka cinye amfanin gonarsu
36Sa’an nan ya karkashe dukan’yan fari a cikin ƙasarsu,
nunan fari na dukan mazantakarsu.
37Ya fitar da Isra’ila, ɗauke da azurfa da zinariya,
kuma daga cikin kabilansu babu wani da ya kāsa.
38Masar ta yi murna sa’ad da suka tafi,
saboda tsoron Isra’ila ya fāɗo musu.
39Ya shimfiɗa girgije kamar mayafi,
da kuma wuta don ta ba su haske da dare.
40Suka roƙa, ya kuwa ba su makware
ya kuma ƙosar da su da abinci daga sama.
41Ya buɗe dutse, sai ruwa ya ɓulɓulo,
kamar kogi ya gudu zuwa cikin hamada.
42Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki
da ya ba wa bawansa Ibrahim.
43Ya fitar da mutanensa da farin ciki,
zaɓaɓɓunsa da sowa ta farin ciki;
44ya ba su ƙasashen al’ummai,
suka kuma sami gādon abin da waɗansu sun sha wahala a kai,
45don su kiyaye farillansa
su kuma kiyaye dokokinsa.
Yabo ga Ubangiji. ▼
▼Da Ibraniyanci Hallelu Ya
Copyright information for
HauSRK