‏ Psalms 106

1Yabi Ubangiji.
Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka kuma a aya 48.

Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

2Wane ne zai furta manyan ayyukan Ubangiji
ko yă furta cikakken yabonsa?
3Masu albarka ne waɗanda suke yin adalci,
waɗanda kullum suke yin abin da yake daidai.

4Ka tuna da ni, ya Ubangiji, sa’ad da ka nuna alheri ga mutanenka,
ka zo ka taimake ni sa’ad da ka cece su,
5don in ji daɗin nasarar zaɓaɓɓunka,
don in sami rabo cikin farin cikin al’ummarka
in kuma shiga gādonka cikin yin yabo.

6Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi;
mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta.
7Sa’ad da kakanninmu suke a Masar,
ba su damu da mu’ujizanka ba;
ba su tuna yawan alheranka ba,
suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku.
8Duk da haka ya cece su saboda sunansa,
don yă sanar da ikonsa mai girma.
9Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe;
ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada.
10Ya cece su daga hannun maƙiyi;
daga hannun abokin gāba ya fanshe su.
11Ruwaye suka rufe abokan gābansu;
babu ko ɗaya da ya tsira.
12Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa
suka kuma rera yabonsa.

13Amma nan da nan suka manta abin da ya yi
ba su kuwa jira shawararsa ba.
14A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su
a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.
15Sai ya ba su abin da suka roƙa,
amma ya aika musu da muguwar cuta.

16A sansani suka ji kishin Musa
da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe.
17Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan
ta binne iyalin Abiram.
18Wuta ta ƙuno a cikin mabiyansu;
harshen wuta ya cinye mugaye.
19A Horeb suka yi ɗan maraƙi
suka yi wa gunkin zubi daga ƙarfe sujada.
20Suka sauke Ɗaukakarsu
saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa.
21Suka manta da Allahn da ya cece su,
wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar,
22mu’ujizai a ƙasar Ham
ayyukan banrazana a Jan Teku.
23Don haka ya ce zai hallaka su,
amma Musa, zaɓaɓɓensa,
ya yi godo a gabansa
don yă kau da hasalarsa daga hallaka su.

24Sai suka rena ƙasa mai ni’ima;
ba su gaskata alkawarinsa ba.
25Suka yi gunaguni a tentunansu
ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba.
26Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu
cewa zai sa su mutu a cikin hamada,
27ya sa zuriyarsu su mutu a cikin al’ummai
ya kuma watsar da su cikin dukan ƙasashe.

28Suka haɗa kai da Ba’al-Feyor
suka kuma ci hadayun da aka miƙa wa allolin da ba su da rai;
29suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu,
sai annoba ta ɓarke a cikinsu.
30Amma Finehas ya miƙe tsaye ya ɗauki mataki,
sai annobar ta daina.
31An ayana masa wannan a matsayin adalci
har zamanai marar matuƙa masu zuwa.
32A ruwan Meriba suka ba Ubangiji fushi,
sai wahala ta zo wa Musa saboda su;
33saboda sun yi tayarwa a kan Ruhun Allah,
har mugayen kalmomi suka fito daga leɓunan Musa.

34Ba su hallakar da mutanen
yadda Ubangiji ya umarce su ba,
35amma suka yi cuɗanya da al’ummai
suka ɗauki al’adunsu.
36Suka yi wa gumakansu sujada,
waɗanda suka zama tarko gare su.
37Suka miƙa’ya’yansu maza hadaya
’yan matansu kuma ga aljanu.
38Suka zub da jini marar laifi,
jinin’ya’yansu maza da mata,
waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana,
ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.
39Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi;
ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci.

40Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa
ya ji ƙyamar gādonsa.
41Ya miƙa su ga al’ummai,
maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu.
42Abokan gābansu suka danne su
suka sa su a ƙarƙashin ikonsu.
43Sau da yawa ya cece su,
amma sun nace su yi tawaye
suka kuma lalace cikin zunubinsu.
44Amma ya lura da wahalarsu
sa’ad da ya ji kukansu;
45saboda su ya tuna da alkawarinsa
kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.
46Ya sa aka ji tausayinsu
a wurin dukan waɗanda suka kame su.

47Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu,
ka kuma tattara mu daga al’ummai,
don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya
mu kuma ɗaukaka cikin yabonka.

48Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,
daga madawwami zuwa madawwami.

Bari dukan mutane su ce, “Amin!”

Yabo ga Ubangiji.
Copyright information for HauSRK