Psalms 107
LITTAFI NA BIYAR
Zabura 107–150
1Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
2Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan,
su da aka fansa daga hannun maƙiyi,
3su da ya tattara daga ƙasashe,
daga gabas da yamma, daga arewa da kudu.
4Waɗansu sun yi ta yawo a jejin hamada,
ba su sami hanya zuwa birnin da za su zauna ba.
5Sun ji yunwa da ƙishirwa,
suka kuma fid da zuciya.
6Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu,
ya kuma cece su daga damuwarsu.
7Ya bishe su ta miƙaƙƙiyar hanya
zuwa birnin da za su zauna.
8Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
9gama yana shayar da masu ƙishirwa
yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.
10Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai,
’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe,
11gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah
suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka.
12Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya;
suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako.
13Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu,
ya kuwa cece su daga damuwarsu.
14Ya fitar da su daga duhu da zurfin ɓaci rai
ya tsintsinke sarƙoƙinsu.
15Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
16gama ya farfashe ƙofofin tagulla
ya kuma ragargaza ƙyamaren ƙarfe.
17Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa
suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.
18Ba su so su ga abinci ba
suka kuwa kai bakin mutuwa.
19Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu,
ya kuwa cece su daga damuwarsu.
20Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su
ya kuɓutar da su daga kabari.
21Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.
22Bari su miƙa hadaya ta godiya
su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki.
23Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa;
su’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.
24Sun ga ayyukan Ubangiji,
ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku.
25Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi
ya ɗaga raƙuman ruwa sama.
26Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa;
a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai.
27Suka yi tangaɗi suna tuntuɓe kamar bugaggu;
suka kuma kai ga ƙarshen dabararsu.
28Sai suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu,
ya kuwa fitar da su daga damuwarsu.
29Ya kwantar da hadiri suka yi tsit;
raƙuman ruwan teku suka yi shiru.
30Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta,
ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai.
31Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa
da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.
32Bari su ɗaukaka shi cikin taron mutane
su kuma yabe shi cikin taron dattawa.
33Ya mai da koguna suka zama hamada,
maɓulɓulai masu gudu suka zama ƙasa mai ƙishirwa,
34ƙasa mai amfani kuma suka zama gishiri marar amfani,
saboda muguntar waɗanda suka zauna a can.
35Ya mai da hamada ya zama tafkunan ruwa
busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulai masu gudu;
36a can ya kai mayunwata su yi zama,
ya kuma samo birnin da za su zauna.
37Suka yi shuka a gonaki suka dasa inabi
suka kuma girbe amfani gona;
38ya albarkace su, yawansu kuma ya ƙaru,
bai kuwa bar garkunansu suka ragu ba.
39Sa’an nan yawansu ya ragu, aka kuma ƙasƙantar da su
ta wurin danniya, bala’i da kuma baƙin ciki;
40shi da yake kawo reni a kan manyan mutane
ya sa suka yi ta yawo a cikin jejin da ba hanya.
41Amma ya fid da mabukata daga wahalarsu
ya kuma ƙara iyalansu da tumakinsu.
42Masu yin gaskiya suka gani suka yi farin ciki
amma dukan mugaye suka rufe bakunansu.
43Duk mai hikima, bari yă ji waɗannan abubuwa
yă kuma lura da ƙauna mai girma ta Ubangiji.
Copyright information for
HauSRK