Psalms 108
Waƙa ce. Zabura ta Dawuda. 1Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah;zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.
2Ku farka, garaya da molo!
Zan farkar da rana.
3Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;
zan rera game da kai cikin mutane.
4Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai;
amincinka ya kai sarari.
5A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai,
bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.
6Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama,
domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.
7Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki,
“Ciki nasara zan raba Shekem
in kuma auna Kwarin Sukkot.
8Gileyad nawa ne, Manasse nawa ne;
Efraim shi hulan kwanona,
Yahuda ne sandana na sarauta.
9Mowab shi ne kwanon wankina,
a kan Edom zan jefa takalmina;
a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”
10Wa zai kawo ni birni mai katanga?
Wa zai jagorance ni zuwa Edom?
11Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu
ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?
12Ka ba mu taimako a kan abokin gāba,
gama taimakon mutum banza ne.
13Tare da Allah za mu yi nasara,
zai kuma tattaka abokan gābanmu.
Copyright information for
HauSRK