Psalms 109
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. 1Ya Allah, wanda nake yabo,kada ka yi shiru,
2gama mugaye da masu ruɗu
sun buɗe bakunansu a kaina;
sun yi magana a kaina da harsunan ƙarya.
3Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni;
sun tasar mini ba dalili.
4A maimakon ƙauna sun sāka mini da zargi,
amma ni mutum ne mai addu’a.
5Sun sāka mini alheri da mugunta,
ƙauna kuma da ƙiyayya.
6Ka naɗa mugun mutum yă yi hamayya da shi;
bari mai zargi yă tsaya a hannun damansa.
7Sa’ad da aka yi masa shari’a, bari a same shi da laifi,
bari kuma addu’o’insa su hukunta shi.
8Bari kwanakinsa su zama kaɗan;
bari wani yă ɗauki wurinsa na shugabanci.
9Bari’ya’yansa su zama marayu
matarsa kuma gwauruwa.
10Bari’ya’yansa su zama masu yawo suna bara;
bari a yi ta koransu daga gidajensu da suke kufai.
11Bari mai binsa bashi yă ƙwace dukan abin da yake da shi;
bari baƙi su washe amfanin aikinsa.
12Bari kada kowa yă yi masa alheri
ko yă ji tausayin marayunsa.
13Bari duk zuriyarsa su mutu,
a shafe sunayensu daga tsara mai zuwa.
14Bari a tuna da laifin kakanninsa a gaban Ubangiji;
bari kada a taɓa shafe zunubin mahaifiyarsa.
15Bari zunubansu su kasance a gaban Ubangiji kullum,
don yă sa a manta da su daga duniya.
16Gama bai taɓa yin tunanin yin alheri ba,
amma ya tsananta wa matalauta
da mabukata da kuma masu fid da zuciya har suka mutu.
17Yana jin daɗin la’antarwa,
bari yă dawo a kansa;
ba ya son sa albarka,
bari kada kowa yă sa masa albarka.
18Ya sa la’antarwa kamar rigarsa;
ta shiga cikin jikinsa kamar ruwa,
cikin ƙasusuwansa kamar mai.
19Bari tă zama kamar mayafin da aka ɗaura kewaye da shi,
kamar ɗamara da aka ɗaura kewaye da shi har abada.
20Bari wannan yă zama sakayyar Ubangiji ga masu zargina,
ga waɗanda suke mugayen maganganu a kaina.
21Amma kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka,
ka yi da ni da kyau saboda sunanka;
ta alherin ƙaunarka, ka cece ni.
22Gama ni matalauci ne mai bukata kuma,
zuciyata kuwa ta yi rauni a cikina.
23Na ɓace kamar inuwar yamma;
ana kakkaɓe ni kamar fāra.
24Gwiwoyina suna mutuwa saboda azumi;
jikina ya rame ba kuma ƙarfi.
25Na zama abin dariya ga masu zargina;
sa’ad da suka gan ni, suka kaɗa kawunansu.
26Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna;
ka cece ni bisa ga ƙaunarka.
27Bari su san cewa hannunka ne,
cewa kai ne, ya Ubangiji, ka yi shi.
28Za su iya la’anta, amma kai za ka sa albarka;
sa’ad da suka tasar za su sha kunya,
amma bawanka zai yi farin ciki.
29Masu zargina za su sha kunya
za a rufe su da kunya kamar mayafi.
30Da bakina zan ɗaukaka Ubangiji sosai;
cikin babban taro zan yabe shi.
31Gama yana tsaya a hannun damar mai bukata,
don yă cece ransa daga waɗanda suke hukunta shi.
Copyright information for
HauSRK