Psalms 11
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don busa. Ta Dawuda. 1A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka.Yaya za ku ce mini,
“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu.
2Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu;
sun kuma ɗana kibiyoyinsu
don su harbi mutanen kirki a zuciya
daga cikin duhu.
3Sa’ad da aka tumɓuke tushe,
me adali zai iya yi?”
4 Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki;
Ubangiji yana a kursiyinsa a sama.
Yana kallon’ya’yan mutane;
idanunsa suna bincike su.
5 Ubangiji yana bincike adalai,
amma ransa yana ƙi mugaye
da masu son rikici.
6A kan mugaye zai zuba
garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu;
iska mai zafi zai zama rabonsu.
7Gama Ubangiji mai adalci ne,
yana ƙaunar gaskiya
masu adalci za su ga fuskarsa.
Copyright information for
HauSRK