‏ Psalms 112

1Yabi Ubangiji.
Da Ibraniyanci Hallelu Ya

Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,
wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.

2’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar;
tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.
3Wadata da arziki suna a cikin gidansa,
adalcinsa zai dawwama har abada.
4Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya,
mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.
Ko kuwa / gama Ubangiji mai alheri ne, mai tausayi da kuma mai adalci.

5Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake,
shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.

6Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba;
za a tuna da mai adalci har abada.
7Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba;
zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.
8Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba;
a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.
9Ya rarraba kyautansa ga matalauta,
adalcinsa zai dawwama har abada;
za a ɗaga ƙahonsa
Ƙaho a nan yana nufin girma.
sama da bangirma.

10Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi,
zai ciza haƙora yă kuma lalace;
sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe.
Copyright information for HauSRK