Psalms 113
1Yabi Ubangiji. ▼▼Da Ibraniyanci Hallelu Ya, haka ma a aya 9.
Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji,
ku yabi sunan Ubangiji.
2Bari a yabi sunan Ubangiji,
yanzu da har abada kuma.
3Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa,
a yabi sunan Ubangiji.
4Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai,
ɗaukakarsa a bisa sammai
5Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu,
Wannan mai zama a kursiyi can bisa,
6wanda yake sunkuya yă dubi
sammai da duniya?
7Yakan tā da matalauta daga ƙura
yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;
8ya zaunar da su tare da sarakuna,
tare da sarakunan mutanensu.
9Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta
ta zama kamar mahaifiyar’ya’ya mai farin ciki.
Yabi Ubangiji.
Copyright information for
HauSRK