‏ Psalms 114

1Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar,
gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe,
2Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah,
Isra’ila mallakarsa.

3Teku ya kalla ya kuma gudu,
Urdun ya juye da baya;
4duwatsu suka yi tsalle kamar raguna,
tuddai kamar tumaki.

5Me ya sa, ya teku, kika gudu,
Ya Urdun, ka juya baya,
6ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna,
ku tuddai, kamar tumaki?

7Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji,
a gaban Allah na Yaƙub,
8wanda ya juye dutse ya zama tafki,
dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.
Copyright information for HauSRK