‏ Psalms 115

1Ba gare mu ba, ya Ubangiji, ba gare mu ba
amma ga sunanka yă sami ɗaukaka,
saboda ƙaunarka da amincinka.

2Me ya sa al’ummai suke cewa,
“Ina Allahnsu?”
3Allahnmu yana a sama;
yana yin duk abin da ya ga dama.
4Amma gumakansu azurfa da zinariya ne,
da hannuwan mutane suka yi.
5Suna da bakuna, amma ba sa magana,
idanu, amma ba sa gani;
6suna da kunnuwa, amma ba sa ji,
hanci, amma ba sa jin ƙanshi
7suna da hannuwa, amma ba sa iya taɓa kome,
ƙafafu, amma ba sa iya tafiya;
ba sa iya ce wani abu da maƙogwaronsu.
8Masu yinsu za su zama kamar su,
haka kuma zai kasance da duk wanda ya dogara da su.

9Ya gidan Isra’ila, ku dogara ga Ubangiji,
shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
10Ya gidan Haruna, ku dogara ga Ubangiji,
shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
11Ku da kuke tsoronsa, ku dogara ga Ubangiji,
shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.

12 Ubangiji yakan tuna da mu zai kuma albarkace mu.
Zai albarkace gidan Isra’ila,
zai albarkace gidan Haruna,
13zai albarkace waɗanda suke tsoron Ubangiji,
manya da ƙanana duka.

14Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru,
da ku da’ya’yanku.
15Bari Ubangiji yă albarkace ku,
shi Mahalicci sama da ƙasa.

16Saman sammai na Ubangiji ne,
amma ya ba da duniya ga mutum.
17Ba matattu ba ne masu yabon Ubangiji,
waɗanda suke gangara zuwa wurin da ake shiru;
18mu ne masu ɗaukaka Ubangiji,
yanzu da har abada kuma.

Yabi Ubangiji.
Da Ibraniyanci Hallelu Ya

Copyright information for HauSRK