‏ Psalms 116

1Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata;
ya ji kukata ta neman jinƙai.
2Domin ya juye kunnensa gare ni,
zan kira gare shi muddin ina da rai.

3Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni,
wahalar kabari sun zo a kaina;
na cika da wahala da ɓacin rai.
4Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce,
“Ya Ubangiji, ka cece ni!”

5 Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci;
Allahnmu yana cike da tausayi.
6 Ubangiji yana tsare masu tawali’u;
sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.

7Ka kwantar da hankali, ya raina,
gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka.

8Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa,
idanuna daga hawaye,
ƙafafuna daga tuntuɓe,
9don in iya tafiya a gaban Ubangiji
a ƙasar masu rai.

10Na gaskata, saboda haka na ce,
“An azabtar da ni ƙwarai.”
11Kuma cikin rikicewana na ce,
“Dukan mutane maƙaryata ne.”

12Yaya zan sāka wa Ubangiji
saboda dukan alherinsa gare ni?

13Zan daga kwaf na ceto
in kuma kira ga sunan Ubangiji.
14Zan cika alkawurana ga Ubangiji
a gaban dukan mutanensa.

15Abu mai daraja a gaban Ubangiji
shi ne mutuwar tsarkakansa.
16Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne;
ni bawanka ne, ɗan baiwarka;
ka’yantar da ni daga sarƙoƙi.

17Zan yi hadayar godiya gare ka
in kuma kira bisa sunan Ubangiji.
18Zan cika alkawurana ga Ubangiji
a gaban dukan mutanensa,
19a filayen gidan Ubangiji,
a tsakiyarki, ya Urushalima.

Yabi Ubangiji.
Da Ibraniyanci Hallelu Ya

Copyright information for HauSRK