Psalms 118
1Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi;ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
2Bari Isra’ila yă ce,
“Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
3Bari gidan Haruna yă ce,
“Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
4Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce,
“Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
5Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji,
ya kuwa amsa ta wurin’yantar da ni.
6 Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai yi mini?
7 Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona.
Zan yi nasara a kan abokan gābana.
8Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga mutum.
9Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga sarakuna.
10Dukan al’ummai sun kewaye ni,
amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
11Sun kewaye ni a kowane gefe,
amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
12Sun rufe ni kamar ƙudan zuma,
amma suka mutu nan da nan kamar ƙayayyuwa masu cin wuta;
a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
13An ture ni baya na kusa fāɗuwa,
amma Ubangiji ya taimake ni.
14 Ubangiji ne ƙarfina da waƙata;
ya zama mai cetona.
15Sowa ta farin ciki da nasara
sun fito a cikin tentunan adalai,
“Hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!
16An ɗaga hannun dama na Ubangiji sama;
hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!”
17Ba zan mutu ba amma zan rayu,
zan kuwa yi shelar abin da Ubangiji ya yi.
18 Ubangiji ya hore ni sosai,
amma bai ba da ni ga mutuwa ba.
19Buɗe mini ƙofofin adalci;
zan shiga in kuma yi godiya ga Ubangiji.
20Wannan ne ƙofar Ubangiji
inda adalai za su shiga.
21Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini;
ka zama mai cetona.
22Zabura Dutsen da magina suka ƙi
ya zama mai amfani;
23 Ubangiji ne ya yi haka,
kuma abu mai daraja ne a idanunmu.
24Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;
bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
25Ya Ubangiji, ka cece mu;
Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.
26Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji.
Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.
27 Ubangiji shi ne Allah
ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu.
Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki
ku kai su ƙahoni na bagade.
28Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya;
kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.
29Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
Copyright information for
HauSRK