‏ Psalms 119

א Alef

1Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi,
waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.
2Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa
suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.
3Ba sa yin wani abin da ba daidai ba;
suna tafiya a hanyoyinsa.
4Ka shimfiɗa farillan
da dole a yi biyayya da su.
5Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne
a yin biyayya da ƙa’idodinka mana!
6Da ba zan sha kunya ba
sa’ad da na lura da dukan umarnanka.
7Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya
yayinda nake koyon dokokinka masu adalci.
8Zan yi biyayya da ƙa’idodinka;
kada ka yashe ni ɗungum.
ב Bet 9Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta?
Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.
10Na neme ka da dukan zuciyata;
kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.
11Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata
don kada in yi maka zunubi.
12Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji;
ka koya mini ƙa’idodinka.
13Da leɓunana na ba da labarin
dukan dokokin da suka fito bakinka.
14Na yi farin ciki da bin farillanka
yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa.
15Na yi tunani a kan farillanka
na kuma lura da hanyoyinka.
16Na yi murna a cikin ƙa’idodinka;
ba zan ƙyale maganarka ba.
ג Gimel 17Ka yi alheri ga bawanka, zan kuwa rayu;
zan yi biyayya da maganarka.
18Ka buɗe idanuna don in iya gani
abubuwan banmamaki a cikin dokarka.
19Ni baƙo ne a duniya;
kada ka ɓoye mini umarnanka.
20Zuciyata ta ƙosa saboda marmari
don dokokinka koyaushe.
21Ka tsawata wa masu fariya, waɗanda suke la’anta
waɗanda kuma suka kauce daga umarnanka.
22Ka cire mini ba’a da reni,
gama ina kiyaye farillanka.
23Ko da yake masu mulki sun zauna tare suna ɓata mini suna,
bawanka zai yi tunani a kan ƙa’idodinka.
24Farillanka ne abin farin cikina;
su ne mashawartana.
ד Dalet 25An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura;
ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
26Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini;
ka koya mini ƙa’idodinka.
27Bari in gane koyarwar farillanka;
sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka.
28Raina ya gaji da baƙin ciki;
ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka.
29Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu;
ka yi mini alheri ta wurin dokokinka.
30Na zaɓi hanyar gaskiya;
na sa zuciyata a kan dokokinka.
31Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji;
kada ka sa in sha kunya.
32Ina gudu a kan hanyar umarnanka,
gama ka’yantar da zuciyata.
ה He 33Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka;
sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe.
34Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka
in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata.
35Ka bi da ni a hanyar umarnanka,
gama a can zan sami farin ciki.
36Ka juye zuciyata wajen farillanka
ba wajen riba ta sonkai ba.
37Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani;
ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
38Ka cika alkawarinka ga bawanka,
saboda a ji tsoronka.
39Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro,
gama dokokinka nagari ne.
40Ina marmarin farillanka ƙwarai!
Ka kiyaye raina cikin adalcinka.
ו Waw 41Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji,
cetonka bisa ga alkawarinka;
42sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina,
gama na dogara ga maganarka.
43Kada ka ƙwace maganarka daga bakina,
gama na sa zuciyata a dokokinka.
44Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka,
har abada abadin.
45Zan yi ta yawo a sake
gama na nemi farillanka.
46Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna
ba kuwa za a kunyata ni ba,
47gama ina farin ciki da umarnanka
saboda ina ƙaunarsu.
48Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna,
ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka.
ז Zayin 49Tuna da maganarka ga bawanka,
gama ka ba ni bege.
50Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce
alkawarinka yana kiyaye raina.
51Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba,
amma ban rabu da dokar ba.
52Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji,
na kuwa sami ta’aziyya a cikinsu.
53Fushi ya kama ni saboda mugaye,
waɗanda suka keta dokokinka.
54Ƙa’idodinka su ne kan waƙata
a duk inda na sauka.
55Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji,
zan kuwa kiyaye dokarka.
56Wannan shi ne na saba yi,
ina yin biyayya da farillanka.
ח Het 57Kai ne rabona, ya Ubangiji;
na yi alkawarin in kiyaye maganarka.
58Na nemi fuskarka da dukan zuciyata;
ka yi mini alheri bisa ga alkawarinka.
59Na lura da hanyoyina
na kuma mayar da matakaina ga farillanka.
60Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba
in yi biyayya da umarnanka.
61Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi,
ba zan manta da dokokinka ba.
62Da tsakar dare nakan tashi in gode maka
saboda dokokinka masu adalci.
63Ni aboki ne ga duk mai tsoronka,
ga duk wanda yake bin farillanka.
64Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji;
ka koya mini ƙa’idodinka.
ט Tet 65Ka yi wa bawanka alheri
bisa ga maganarka, ya Ubangiji.
66Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau,
gama na gaskata a umarnanka.
67Kafin in sha wahala na kauce,
amma yanzu ina biyayya da maganarka.
68Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau;
ka koya mini ƙa’idodinka.
69Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi,
na kiyaye farillanka da dukan zuciyata.
70Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi
amma ina farin ciki a dokarka.
71Ya yi kyau da na sha wahala
don in koyi ƙa’idodinka.
72Doka daga bakinka ya fi mini daraja
fiye da azurfa da zinariya guda dubu.
י Yod 73Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni;
ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka.
74Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni,
gama na sa zuciyata a maganarka.
75Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne,
kuma cikin aminci ka hore ni.
76Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya,
bisa ga alkawarinka ga bawanka.
77Bari tausayinka yă zo mini don in rayu,
gama dokarka ce farin cikina.
78Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili;
amma zan yi tunani a kan farillanka.
79Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni,
waɗanda suka gane da farillanka.
80Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka,
don kada in sha kunya.
כ Kaf 81Raina ya tafke da marmari don cetonka,
amma na sa zuciyata a maganarka.
82Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka;
Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?”
83Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi,
ban manta da ƙa’idodinka ba.
84Har yaushe bawanka zai yi ta jira?
Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini?
85Masu girman kai sun haƙa mini rami,
sun ƙetare dokarka.
86Dukan umarnanka abin dogara ne;
ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili.
87Sun kusa gama da ni a duniya,
amma ban bar bin farillanka ba.
88Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka,
zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka.
ל Lamed 89Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce;
tana nan daram a cikin sammai.
90Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai;
ka kafa duniya ta kuma dawwama.
91Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau,
gama dukan abubuwa suna maka hidima.
92Da ba don dokarka ce farin cikina ba,
da na hallaka a cikin azabana.
93Ba zan taɓa manta da farillanka ba,
gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina.
94Ka cece ni, gama ni naka ne;
na yi ƙoƙarin neman farillanka.
95Mugaye suna jira su hallaka ni,
amma zan yi ta tunani a kan farillanka.
96Ga duk cikakke na ga kāsawa;
amma umarnanka ba su da iyaka.
מ Mem 97Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka!
Ina tunani a kanta dukan yini.
98Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana,
gama kullum suna tare da ni.
99Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina,
gama ina tunani a kan farillanka.
100Ina da ganewa fiye da dattawa,
gama ina biyayya da farillanka.
101Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya
domin in yi biyayya da maganarka.
102Ban rabu da dokokinka ba,
gama kai da kanka ne ka koya mini.
103Ɗanɗanon maganarka akwai zaki,
sun ma fi zuma zaki a bakina!
104Na sami ganewa daga farillanka;
saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba.
נ Nun 105Maganarka fitila ce ga ƙafafuna
haske kuma a kan hanyata.
106Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi,
cewa zan bi dokokinka masu adalci.
107Na sha wahala sosai;
ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka.
108Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji,
ka kuwa koya mini dokokinka.
109Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana,
ba zan manta da dokarka ba.
110Mugaye sun kafa mini tarko,
amma ban kauce daga farillanka ba.
111Farillanka su ne gādona har abada;
su ne farin cikin zuciyata.
112Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka
har ƙarshe.
ס Samek 113Na ƙi mutane masu baki biyu,
amma ina ƙauna dokarka.
114Kai ne mafakata da garkuwata;
na sa zuciyata a maganarka.
115Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta,
don in kiyaye umarnan Allahna!
116Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu;
kada ka bari a gwale sa zuciyata.
117Ka riƙe ni za a kuma cece ni;
kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci.
118Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka,
gama yaudararsu banza ne.
119Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti;
saboda haka nake ƙaunar farillanka.
120Naman jikina na rawan jiki don tsoronka;
na cika da tsoron dokokinka.
ע Ayin 121Na aikata abin da yake mai adalci da kuma daidai;
kada ka ni a hannun masu danne ni.
122Ka tabbatar da lafiyar bawanka;
kada ka bar masu girman kai su danne ni.
123Idanuna sun gaji, da jiran cetonka,
da jiran alkawarinka mai adalci.
124Ka yi da bawanka bisa ga ƙaunarka
ka kuma koya mini ƙa’idodinka.
125Ni bawanka ne, ka ba ni fahimi
don in gane farillanka.
126Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji;
ana karya dokarka.
127Saboda ina ƙaunar umarnanka
fiye da zinariya, kai, fiye da zinariya zalla,
128saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau,
na ƙi kowace hanyar da ba daidai ba.
פ Fe 129Farillanka masu banmamaki ne;
saboda haka nake yin biyayya da su.
130Fassarar maganganunka sukan ba da haske;
sukan ba da ganewa ga marar ilimi.
131Ina hakkin da bakina a buɗe,
ina marmarin umarnanka.
132Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai,
yadda kullum ka yi wa waɗanda suke ƙaunar sunanka.
133Ka bi da sawuna bisa ga maganarka;
kada ka bar zunubi yă mallake ni.
134Ka fanshe ni daga mutane masu danniya,
don in yi biyayya da farillanka.
135Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka
ka kuma koya mini ƙa’idodinka.
136Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi,
gama ba a biyayya da dokarka.
צ Tsade 137Mai adalci ne kai, ya Ubangiji,
dokokinka kuma daidai ne.
138Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne;
su kuma abin dogara ne ƙwarai.
139Kishina ya cinye ni ɗungum,
gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka.
140An gwada alkawuranka sarai,
bawanka kuwa yana ƙaunarsu.
141Ko da yake ni ba kome ba ne an kuwa rena ni,
ba na manta da farillanka.
142Adalcinka dawwammame ne
dokar kuma gaskiya ce.
143Wahala da damuwa suna a kaina,
amma umarnanka su ne farin cikina.
144Farillanka daidai ne har abada;
ka ba ni ganewa don in rayu.
ק Kof 145Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji,
zan kuwa yi biyayya da ƙa’idodinka.
146Na yi kira gare ka; ka cece ni
zan kuwa kiyaye farillanka.
147Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako;
na sa zuciyata a maganarka.
148Ban rufe idanuna ba dukan dare,
don in yi tunani a kan alkawuranka.
149Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka;
ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga dokokinka.
150Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa,
amma suna nesa da dokarka.
151Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji,
kuma dukan umarnanka gaskiya ne.
152Tun tuni na koyi daga farillanka
cewa ka kafa su su kasance har abada.
ר Resh 153Ka dubi wahalata ka cece ni,
gama ban manta da dokarka ba.
154Ka kāre manufata ka kuma fanshe ni,
ka cece rai na kamar yadda ka alkawarta!
155Ceto yana nesa da mugaye,
gama ba sa neman ƙa’idodinka.
156Tausayinka da girma yake, ya Ubangiji;
ka kiyaye raina bisa ga dokokinka.
157Maƙiya masu yawa ne suke tsananta mini,
amma ban rabu da farillanka ba.
158Na dubi marasa aminci da ƙyama,
gama ba sa yin biyayya da maganarka.
159Dubi yadda nake ƙaunar farillanka;
ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga ƙaunarka.
160Dukan maganganunka gaskiya ne;
dukan dokokinka masu adalci madawwami ne.
ש Sin da Shin 161Masu mulki suna tsananta mini ba dalili,
amma zuciyata na rawan jiki game da maganarka.
162Ina farin ciki da alkawarinka
kamar yadda wani kan sami ganima mai girma.
163Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya
amma ina ƙaunar dokarka.
164Sau bakwai a rana ina yabonka
saboda dokokinka masu adalci.
165Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama,
kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe.
166Ina jiran cetonka, ya Ubangiji,
ina kuma bin umarnanka.
167Ina biyayya da farillanka,
gama ina ƙaunarsu ƙwarai.
168Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka,
gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka.
ת Taw 169Bari kukata ta zo gare ka, ya Ubangiji;
ka ba ni ganewa bisa ga maganarka.
170Bari roƙona yă zo gabanka;
ka cece ni bisa ga alkawarinka.
171Bari leɓunana su cika da yabonka,
gama ka koya mini ƙa’idodinka.
172Bari harshena yă rera game da maganarka,
gama dukan umarnanka masu adalci ne.
173Bari hannunka yă kasance a shirye don yă taimake ni,
gama na zaɓi farillanka.
174Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji,
dokarka kuwa ita ce farin cikina.
175Bari in rayu don in yabe ka,
bari kuma dokokinka su raya ni.
176Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya.
Ka nemi bawanka,
gama ban manta da umarnanka ba.
Copyright information for HauSRK