‏ Psalms 12

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit.
Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce.
Zabura ta Dawuda.

1Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma;
masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.
2Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya;
zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce
suna cike da ruɗu a zukatansu.

3Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu
da kuma kowane harshe mai fariya,
4masu cewa,
“Da harsunanmu za mu yi nasara;
leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”

5“Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata,
zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji.
“Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”
6Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure,
kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu,
aka tsabtacce sau bakwai.

7Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya
ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.
8Mugaye suna yawo a sake
sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.
Copyright information for HauSRK