Psalms 120
Waƙar haurawa. 1Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata,ya kuwa amsa mini.
2Ka cece ni, ya Ubangiji,
daga leɓuna masu ƙarya
da kuma daga harsuna masu yaudara.
3Me zai yi maka,
me kuma ya fi,
ya kai harshe mai yaudara?
4Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi,
tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.
5Kaitona da nake zama a Meshek,
da nake zama a ciki tentunan Kedar!
6Da daɗewa na zauna
a cikin waɗanda suke ƙin salama.
7Ni mutum ne mai salama;
amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.
Copyright information for
HauSRK