‏ Psalms 121

Waƙar haurawa.

1Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,
ta ina ne taimakona zai zo?
2Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,
wanda ya kafa sama da ƙasa.

3Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,
shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;
4tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila
ba ya gyangyaɗi ko barci.

5 Ubangiji yana tsaronka,
Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;
6rana ba za tă buge ka cikin yini ba
balle wata da dare.

7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,
zai tsare ranka;
8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka
yanzu da har abada kuma.
Copyright information for HauSRK