‏ Psalms 125

Waƙar haurawa.

1Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,
wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.
2Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,
haka Ubangiji ya kewaye mutanensa
yanzu da har abada kuma.

3Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance
a kan ƙasar da take rabon adalai ba,
domin kada masu adalci su yi amfani
da hannuwansu su aikata mugunta.

4Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu,
ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.
5Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi
Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta.

Salama tă kasance tare da Isra’ila.
Copyright information for HauSRK