‏ Psalms 126

Waƙar haurawa.

1Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona,
mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.
2Bakunanmu sun cika da dariya,
harsunanmu da waƙoƙin farin ciki.
Sai ana faɗi a cikin al’ummai,
Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”
3 Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu,
mun kuwa cika da farin ciki.

4Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji
kamar rafuffuka a Negeb.
5Waɗanda suka yi shuka da hawaye
za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.
6Shi da ya fita yana kuka,
riƙe da iri don shuki,
zai dawo da waƙoƙin farin ciki,
ɗauke da dammuna.
Copyright information for HauSRK