‏ Psalms 128

Waƙar haurawa.

1Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,
waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
2Za ka ci amfanin aikinka;
albarku da wadata za su zama naka.
3Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai’ya’ya
a cikin gidanka;
’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun
kewaye da teburinka.
4Ta haka mai albarka yake
wanda yake tsoron Ubangiji.

5Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona
dukan kwanakin ranka;
bari ka ga wadatar Urushalima,
6bari kuma ka rayu ka ga’ya’ya’ya’yanka.
Salama tă kasance tare da Isra’ila.
Copyright information for HauSRK